FITILAR HASKA ZUCIYAR MASOYI

....SAKON HASAKA ZUCIYAR MASOYI....



Haske kan bayyana a dausayin zuciya a yayin da duhu ke gaggawar ficewa daga gare ta ba tare da ba ta lokaci ba....Kafin zuciya ta kafa tutar samun nasarar cafke ragamar son wanda take so, za ka same ta ne tsundum cikin duhu mai tsanani sakamakon rashin samun mai yayyafa mata feshin sinadarin so a gonar ruhi....


 Ruhin dan-adam yana kasancewa ne cikin wani irin yanayi na kwadayin samun mai kula da shi a kowan ne lokaci, wannan dalilin ne ya sa zuciya ke tsananin son duk mai kyautata mata da kuma kin duk mai takura mata..... 


Kasancewar zuciya ita ce tubalin ruhi sannan kuma na'urar dake kimtsa soye- soyen ruhi,sannan kuma 


ma'adanar sirri, tana kasancewa ne a cikin wani irin yanayi mai hasken gaske da zarar ruhi ya sami abin da yake muradi....  


Tsananin hasken zuciya yana tasiri matuka dan kuwa har fuska tana iya bayyana wa da zarar ka ga wadda ke cikin shaukin so nan take za ka iya ganewa.











Duban masoya : a lokacin da masoya biyu suka kasance tare akwai wani irin satar kallo da masoya ke ai watar wa a tsakanin su, kallo ne mai girgiza zuciya har sai zuciya ta kakkabar da duk wata damuwa da ta makale a jikinta. Hakika kallon yakan sanyaya 


zuciya matukar sanya yawa musamman idan an cakuda kallon da kalaman so masu gigita wanda aka yi dominsa.... 


A lokacin ne masoya za su ji tamkar su kadai ne a duniya saboda tsananin farin ciki da ya da baibaye zuciyarsu, gami da tsananin haske tamkar farin zinare wanda aka ajiye shi a hasken farin wata.... 


Hasken zuciyar masoya a irin wannan yanayi wa ne hasken walkiya, domin ita walkiya haskawa daya take yi ta bace, amma zuciyar masoya kuwa hasken zai kasance zaunanne a ruhi tsawon zamani. Mhm! Soyayya hasken rayuwa, rashin soyayya kuwa kuncin rayuwa...


Shin wai ma a rayuwa akwai abin da ya fi soyayya dadi kuwa? Amma fa soyayyar da aka kafa gininta da tubalin gaskiya ne kadai hakan ke faruwa....

Post a Comment

Previous Post Next Post