HANYOYIN DA ZAKIBI DOMIN MALLAKAR MIJINKI.
1. Ki riqa yi masa halin mata, wato irinsu kisisina, shagwaba dss, don namiji baya son mai halin maza ta zama matarsa.
2. Ki zamo mai iya kwalliya. Idan kin kasance mai zaman gida ce to kici ado ko da kuwa baza ki fita ko zuwa ko ina ba.
3. Kada ki fara lissafowa mijinki matsalolinki ko na gida a lokacin da ya shigo, ki barshi ya huta tukuna ya samu nutsuwa.
4. Ki zamo mai kirki, ladabi da biyayya ga Mahaifiyar mijinki kamar yadda zaki so shima ya zamo kamar haka ga mahaifiyarki.
5. Ki dinga qarawa mijinki qarfin gwiwa akan abinda kika ga alamar yana nema ya karaya, hakan zai sa ya gwarzo a cikin maza.
6. Ki dinga fadawa mijinki cewa kina sonshi sau dayawa, dayawa dayawa, Aisha رضالله عنها tace Annabin tsira SAW ya kasance yana tambayarta qarfin soyayyarta gareshi, sai tace mishi kamar ‘zarge’ (wato dauri ko kulli wanta bazai kwance ba), sai ya sake tambayarta ‘yaya zargen yake’? Kuma ya kasance yana cewa da ita Allah ya saka miki da alkhairi Aisha, ina farin ciki da jin dadi dake fiye da yadda kike farin ciki dani!
7. Ki dinga yawan sada zumunci ga mutanen gidansu (kamar ziyartarsu, kiransu a waya dss).
8. Ki dinga bashi wani dan qaramin aiki a gida; kuma idan yayi aikin sai ki gode masa. Hakan zai sa ya qara dagewa.
9. Ki dinga qarfafa masa zuciya wajen yin aikin alheri
10. Idan yana cikin damuwa ki dan bashi lokaci, da yardar Allah sai kiga ya dawo dai dai.
11. Ki dinga yi masa godiya akan sama miki abinci da muhalli da yake yi, abune mai girma!
12. Ki tuna cewa mijinki ma yana da damuwa da farin ciki, saboda haka ki dinga tunawa dashi wajen yanke hukunci.
13. Idan mijinki ya nuna damuwa akan dan qaramin abu da kika yi masa to sai ki bashi haquri kuma ki dena.
14. Kiyi dukkan abubuwan da aka lissafo saboda Allah, sai kiga Allah ya sa miki albarka a cikin duk abinda kike yi.
Allah ya kawo mana albarka da yalwar arziqi da ta ‘ya’ya a cikin Rayuwar Aure!