MA'ANAR AURE.
Abinda aka sani da aure a dukkan al’adu, yaruka da addinai shine namiji ya samu macen da yake, ya jawo hankalinta akan ta yarda suyi zaman tare, ya biya haqqoqinta sannan mutane su shaida akan cewa ta zama matarsa saboda haka an halatta masa yin duk wasu abubuwa da kan iya gudana tsakanin mace da namiji. Yana daga cikin al’adun kuma cewa daga ranar ita macen zata bar gidansu ta koma gidan shi wanda ta zaba kuma ta aura a matsayin mijin nata.
Akan daura aure tare sharudda da yawa wandanda suka banbanta daga al’ada zuwa al’ada. A al’ada da addini na bahaushe, sharuddan da sukan biyo aure sun hada da samarda muhalli ko gurin zama ga matar, ciyar da ita, sama mata tufafi da kuma kula da lafiyarta.
Dalilin Yin Aure
Akwai dalilai da yawa da suka sa dole duk wani mutum mai hankali yayi aure idan yakai munzalin yin auren. Annabin tsira (S.A.W) yace da al’ummarsa kuyi aure ku hayayyafa dan inyi alfahari da yawanku ranar qiyama. Sannan Allah SWT ya halicci mutane (maza da mata) da sha’awa, wacce hanya daya da duk addinai suka yarda da ayi amfani da ita wajen biyan buqatar sha’awa shine aure. Wadannan dalilai guda biyu ma kawai sun isa hujja ga masu cewa su basa soyayya; sai da soyayya ne za’a iya yin aure.
Idan aka duba bangaren ibada kuma, Annabi (S.A.W) yace wanda yai aure ya bayar da rabin ibadarsa, sannan duk wani abu da masu aure zasu yiwa junansu na daga jin dadi lada zasu samu, hmn wannan itace garabasa, hanya mai sauqi ta samun aljanna.
Yana da amfani mutum yasan wadannan manufofi na yin aure kafin yayi aure, sannan kuma ya dinga tuna su koda yaushe, musamman a lokacin da aka samu sabani, hakan zai taimaka wajen shawo kan da yawa daga cikin matsalolin aure. Haka shima wanda yaje yin sulhu ga ma’auratan da suka sami sabani, yana da kyau ya tunantar dasu akan wadannan manufofi na yin aure; Allah yasa mu dace.