MECECE SOYAYYA??

 MECECE SOYAYYA??




SOYAYYA ita ce tushen rayuwa mai inganci da ke kawo zaman lafiya a cikin rayuwar mu ta yau da kullum, ka so mai son ka.

MECE CE SOYAYYA?

Wannan tambaya an dad’e ana kaiwa da kawowa a kanta, masana da yawa sun tattauna domin ganin sun samar da ma’anarta domin a gane ta a kuma fahimce ta. Kamar haka:

Soyayya ita ce nuna ‘kauna daga 6angarori biyu na masu ‘kaunar juna (C.N.H.N.).

Muhammad Hashimu ya bayyana cewa: ‘Soyayya ita ce ni’ima mafi d’aukaka da Allah Ya ba wa bayinsa. Soyayya ita ce zuciyoyi biyu a dun’kule su cure, su game cikin zuciya d’aya. Haka kuma soyayya ita ce rai biyu cikin jiki d’aya. Soyayya ita ce mutum biyu cikin mutum d’aya. Abin da ake nufi a nan shi ne, idan mutum ya so wani tsananin soyayya sai ya zama cewa koda yaushe cikin tunaninsa yake, ba ya damuwa da kowa sai shi, ba ya son ji da ganin kowa sai shi, wato kenan sun zama mutum d’aya cikin jiki biyu.’

Duk da abubuwan da muka ambata hakan ba zai sanya mu ce mun bayyana ha’ki’kanin ma’anar soyayya ba. Domin ita soyayya ba za a iya siffanta yadda take ba. Sai mutum ya shige ta, sannan zai san ta.

NAN ZAKA DANNA KA KALLI VIDEO 👇👇👇👇👇



KASHE-KASHEN SOYAYYA.

Soyayya ta kasu izuwa gida uku kamar haka:

1 Soyayya Don Sha’awa.

2 Soyayya Don Abin Duniya.

3 Soyayya Ta Ha’ki’ka Ko Gaskiya.

1-SOYAYYA DON SHA’AWA: A wani lokaci mace kan ga namiji ko kuma namiji ya ga mace, sai d’aya daga cikinsu ya ga wani abu a jikin d’ayan har ya ja hankalinsa ya ba shi sha’awa, ya ji yana son wannan mutum saboda wannan abu. To irin wannan ba soyayya bace sha’awa ce da zarar d’aya daga ciki ya biya bu’katar tashi sai a fara neman hanyar rabuwa da juna.

2-SOYAYYA DON ABUN DUNIYA: Irin wannan soyayya Ita ce wadda ake yi don kud’i, ko dan kyau ko dan wani ‘kyale-‘kyalen duniya. Ita ma irin wannan soyayya ba ta cika nisa ba, da zarar abun da ake yin soyayyar dan shi ya gushe, sai a fara shirye-shiryen nesanta da juna.

3-SOYAYYA TA HAK’IK’A KO GASKIYA: Irin wannan soyayya ita ce wadda ake amfani da hankali da tinani wajen kafa ta. Duk soyayyar da ba a gina ta a kan sha’awa ko wani abun duniya, ko wani mugun nufi ba, to wannan soyayya ta gaskiya ce. Kuma ita ce irin soyayyar da take d’orewa wadda ba ta yankewa har abada.

DANNA NAN DOMIN KOLLON CIKAKKUN FINA FINAN MU 👇👇👇👇👇👇👇



Post a Comment

Previous Post Next Post