MENENE SO DA KAUNA.

 MENENE SO DA KAUNA.

 


So da kauna, wani shauki/hali ne wanda ke kama da juna wurin tantancesa a ilimance, haka kuma a aikace .

 Ka santuwar cewa ba kowa ke sanin abunda yake aikatawa ba a tsakanin mu, ko kuma, me masoyina masoyiyata ke yi man daga cikin wannan halaye. Kowannen anayinsu ne ba tare da mutum yasan me yake aikatawa ba, kasancewar baya iya tantancewa tsakanin biyun nan me suke nufi. Ko wannen su aikatasu halal ne a addinin muslumci, saidai wani yafi wani, daraja a idan shari'a kasancewar muhimmancin sa da amfaninsa tsakanin masoya. Hmm nasan wasu zasuyi mamaki akan cewar me ya hada addini da soyayya, tirqashi... To ka sani Madarar da zumur ilimin soyayya tatacce daga addinin muslunci, yake. Haka kuma duk wanda yabi tsarin soyayya a muslumci, ba shakka zai yi soyayya wacce take tatatta, kuma amintatta. Wacce babu yaurada ko ha'incin juna tsakanin masoya. 

 

Menene Kauna?

= Kauna tamkar SO take sai daifa tafi So aminci, domin ita kauna bata canzawa, kuma ita kauna ba’a amutu akanta, ma’ana ba’acewa lallai sai an auri wanda ake Kauna ko sai an kasance tare dashi, in hakan bata yuwuba za’ai tashin hankali, ko a fara zargin shi abin kaunar, ita kauna ba haka takeba, ko anyi nasarar samun abin kaunar ko ba’ayiba, ana cigaba da masa fatan alheri kamar yadda kake masa a baya. Kuma ita kauna bata kwaranyewa, rashin haduwa tsawan zamani bai kwaranyar da ita.

Galibi abinda ke kawo kauna dabi’une, wato halaiyan abin kaunar suke janyo zuciya zuwa ga kaunarshi.

 

 

1. SO ne sinadarin dake sanyaya zuciya kamar yadda freezer ke sanyaya zazzafan ruwa zuwa kankara.

2. SO ne tsuntsun dake kaikawo tsakanin zukata mabanbanta daga karshe har sai ya sami zuciyar da zai gina shekarsa.

3. SO ne dausayin farin ciki mai haddasa ruruwar farin ciki mara misali.

4. SO ne siffar samin ingantacciyar rayuwa mai alfanu.

5. SO ne tsaunin rahama mai sanya masoya magagi gami da shantakewa a bisa tagwayen manufofi.

6. SO ne fitilar dake haskaka zuci yayinda ta fada cikin duhu matsananci.

7. SO ne tekun dake gudana tsakanin zukata mabanbanta.

8. SO ne asalin rayuwa, sannan kuma abin dake sarrafa ragamar dokin rayuwa a bisa hanya managarciya.

9. SO ne mafarar kauna, sai so ya sami kyakkyawan mazauni a zuci kafin kauna ta biyo bayansa.

10. SO ne bishiyar dake tsirowa a dausayin zuci, mai fitar da furanni kyawawa masu kyawun gani.

11. SO ne sadaukin zuci, mai ingiza zuciya filin dagar kauna, har sai ya kafa tutarsa a bainar zuciya.

12. SO ne ginshiki, sannan kuma tubalin kauna sai an kafa tubalin so a zuci kafin ginin kauna ya tabbata a matabbatar ruhi.

13. SO ne tekun dake gangarowa daga ruhi zuwa sassa daban-daban na jiki, wanda ke fesar da shauki a nahiyar kalbi.

14. SO ne maganin dake warkar da zuciyar data shiga garari.

15. SO ne guguwar dake daukar, masoya, idan guguwar so ta dauki masoya takan makantar da idanuwansu har su rasa ganin laifin juna.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post