SAKON KWANTAR D HANKALINA MACE

®®® GA SAKON KONTAR DA HANKALI AGAREKI MASOYIYATA ®®®



Jinjina mai dauke da sarautar girma da cikakken iko a gareki ma'abociyar haske da kyawun kwalliya,

da fatan kina cikin kyakkyawan yanayin walwala da kwanciyar hankali,

ba shakkan duniyar masoya tayi ninkaya da tabbacin kece mafi cancanta da ki mallaki masarautar fadar duniyar masoya,

hmm sahibata matsayinki ya zarce matsayin yar sarki domin na kasance sariki mai fadawa da rigar yaki acikin, 

masarautar fadar zuciyar ki hakan yasa ko antara goma zan dauki daya acikin jerin yan matan birni da kauyuka shiyasa nake tattalinki ta hanyar kwatanta maki soyayyar gadkiya

 daga lokacin da muka kafa harsashin soyayyar mu ya zuwa yanzu nake sanya kaina cikin maza mafi sa'ar rayuwa.

domin kuwa ni kadai ne nayi dace da masoyiyar asali watau ke zuciyata ta dade da narkewa cikin kogin sonki begenki ne makamashin dake kara rura wutar sonki acikin zuciyata .

hmm Sahibata idan batare dake ba rayuwata bazata iya aiwatar da komai ba, 

domin da zaki samu ganin wani babban gurbi acikin zuciyata da babu abin da zakigani ya samu masauki na musamman face soyayyar ki.

idan da zai zamo akwai Wata 'ya mace da zan daukaka darajar soyayyarta zuwa kololuwar sama ,

 to da kece kikafi cancanta domin sonki shine farin cikin rayuwata.

Fatana ya zamo murmushin ki shine sinadarin bayyanar kyakkyawar annurin hasken dake shimfide a saman kyakkyawar fuskarki wassalam:kihuta lafiya Sahibata. 

MU KASANCE DAKU A CIKIN SHIRI NA GABA

MUNGODE 🙏

Post a Comment

Previous Post Next Post