KI TATTALA SOYAYYATA.....
____Arzikin Abinda Baki Ya Furto Cikin Yanayin Sigar Zancen Masoya Suna Samun Masaukine Acikin Masaukan Da Aka Tanadesu Musamman Domin Girmama Sarauniya Irinki_
__Kyawun Daidaituwar Halittarki Sun Riski Kyawun Nasaba Da Kwarjinin Sarautar Kyawawa Sune Suka Hadu Wajen Inganta Komai Naki Wanda Ya Zarce Halittar Dukkan Wasu Yan Mata
____Sanadin So Shine Alkawarin Masoya Wanda Muka Dauka Tun Ranar Damukai Musanyar Kalaman Kauna Tsakanin Ni Dake
Amincin Allah Agareki Ya Annurin Haske Makusancin dake Kawatar Da Ruhin Zuciyar Dake Miki Soyayyar Gaskiya Wadda Batada Karshe
___Mai Sonki Ne Akowace Rana Shine Ya Sake Sulalowa Da Wani Sabon Sakon Sautin So Wanda Ya Mamayi Dukkan Wani Sassan Jikina
__Na Tsara Abun Dana Tsara Ne Akan Tsari Domin Suzo Cikin Nutsuwar Da Zasuyi Ladabin Gaisheda Kyakkyawar Sarauniya Irinki
____Sonki Ne Yake Kara Tunzurani Banajin Kira Sannan Bazan Razana Ba Kowane Lokaci Sautin Muryarki Shine Abunda Yake Kara Wadatar Da Farin Cikina
___Barkanki Da Muhimmin Lokaci Irin Wannan Ina Mai Cike Da Farin Cikin Ganin Sassanyar Murmushinki Yana Bayyanuwa Adaidai Wannan Lokaci Dakike Karanta Sakon Zuciyata
___Adadin Abinda Ake Kididdigawa Akan Kyau Ya Wuce Adadin Lissafin Bugawar Numfashin Ruhi Alokacinda Ya Tunkari Muradin Ransa
___Kin Iya Komai Na Masoya Nayi Godiya Ga Allah Mai Wadata Bawa Da Komai Wanda Cikin Ikonsa Ne Dakuma Lamuninsa Ya Mallakamin Nagartacciyar Masoyiya Irinki