SAKON SOYAYYA PART (3)

SIRRIN MURYA A SOYAYYA.



Murya wata abace wacce dukkan masoyan da suka rasata,to a zahirin gaskiya sun rasa babban abu acikin soyayyar su.

Domin kuwa ita murya itace wacce take daya daga cikin Abubuwan dake sanya masoyi ya ringa kewarka.

A duk lokacin da ba kwa tare dashi.

Hakika muray wata abace mai matukàr tasiri a zuciyar masoya.

Domin A kalla tana da kaso 30% cikin 💯 A bangaren soyayya.


Wata babbar ka'idace da take kara

inganci da

tasirin kalaman bayyana soyayya

tsakanin

masoya ita ce, yanayi da sigar da kalamanke fita su isa kunnen mai sauraren su.

Dole sai masoya sun rika sarrafa murya wajenbayyana shaukin kaunarsu ga juna;


kowane kalami da irin sigar muryar da tafi

dacewa

da

shlaman nuna so da kauna ana furta su

gauraye da shaukin bege, cikin

bayyanannun kalmomi, wani sa'in ana iya furta

su cikin

yanayin wake, ko a siririntar da murya ko

a

nauyaya ta don ta yi daidai da lokaci da

kuma

yanayi.

Kalaman tausayawa, suna bukatar a

tausasa murya wajen furta su, a cakuda

murya kafin a bayyana jimamin abin da

ake

tausayawa dominsa.


Kalaman ban hakuri na bukatar a nauyaya

su da muryar da-na-sani, nadama da

marairaicewa.


Kalamana godiya na bukatar a kawata

furucinsu da farin ciki da jin dadin abin

da ake godewar.


Kalaman wasa da zaurance kuwa sai a

surka muryarsu da jin dadi da nishadi.


Kalaman sha'awa, ko dai a sa murya ta

yi

taushi yayin furucinsu, ko a sanyaya ta, ko a

siririnta murya, ko a sa murya ta yi kasa-

kasa,

ko a rika fitar da kalaman cikin rada, ko a

rika

fitar da su dai-dai cikin yanayi na jan hankali;

abin nufi dai, masoya su yi kokari su rika

karya murya cikin siga mafi dacewa da

lokaci

da kuma yanayi.


Kalaman sha'awa ba

lallai sai sun yi ma'ana ba wata sa'in, ana iya

caccakuda wasu kalmomi a fitar da su da

wani irin karin muryar sha'awa wadanda

zai

sa su yi tasiri sosai.


Kalaman neman alfarma sai a gauraya su

da muryar kwantar da kai da

marairaicewa.


 


Ku saurare mu a kalaman soyayya part 4

Mungode.........

1 Comments

Previous Post Next Post