SOYAYYAR KI TANA RAINA
Aminci Allah a gareki ya fitilar haskaka zuciyata da ruhina,
yarda cikin salama fatana su kasance amintattu a cikin zuciyarki Nurul Qalbiy.
Sweetyna bude kunnin ki kiji dadaden kalaman soyayyar da suke Kara bayyana irin tasirin soyayyarki.
daga bakin mai martaba sarkin masarautar fadar zuciyarki
Masoyiyata sahibata jarumata, uhmmmm, gimbiyata.
ko kinsan cewa soyayyar ki a cikin zuciyata ta kasance tamkar wata tsoka a cikin jikina ne ?
wacce idan ta cire Zan iya samun tawaya , rayuwarta batare dake ba , tamkar rayuwar kurkuku ce da babu walwala a cikin sa.
Ya ma'abociyar haske "a duk lokacin da naji sautin muryarki , hakan yana saka ni a cikin farinciki idan Kuma ina kallon kyakkyawar fuskarki ,babu abin da nafi Qauna fiye da tattausan murmushinki ma'abocin daukar hankali.
my Love' yaushe ne zan gaji da kallon kyakkyawar fuskarki?
Yaushe ne zan iya hakuri ba tare da naji zazzakar muryarki ba ?
Yaushe ne zan iya hakuri idan wani rabani dake ?
Ko kadan bazan iya bari ki kubuce min ba " kece mahadin rayuwata.
Masoyiyata hakika na kasance tamkar jariri a soyayyar ki.
ina abukatar a kula dani, a rarrashe ni saboda ina gudun halin da zan shiga idan har kika gujeni ko Kika rabu dani, zan zamo Dan marayar masoya.
Baby na " babu wani lokaci da nake kasancewa a cikin sa face soyayyar ki tana cikin zuciyata.
hatta nunfashina Yana kasancewa ne tare da Kaunar ki a cikin Ruhina.
Da ace zan bude maki zuciyata ki kalli cikin ta ,tabbas da sai kin tabbatar da cewa babu wani da namiji da yake yi maki irin so da Kaunar dana shimfida a gareki.
*uhuhmm ubby na nayi alkawarin soyayyata a gareki sadaukarwa ce ta har abada ,babu Kuma mai iya rabani dake sai mutuwa. By SANATAN MASOYA
INA SONKI.
KUJIRAMU A CIKIN SHIRI NA GABA WATO SAKON SOYAYYA PART (5).
MUNGODE..