SAKON SOYAYYA PART (5) RARRASHI A SO.

RARRASHI A SOYAYYA.



Hakikanin gaskiya Rarrashi A Tsakanin Masoya Yana Da Muhimmanci Da Tasiri Ga Rayuwar Soyayyar Ku. 

 Yiwa juna laiphi wannan abune da bai tsallake kan kowa ba, kasa a ranka a koda yaushe zaka iya tsintar kanka cikin.

 rarrashin abin so da ƙaunarka abisa ajizanci na dan Adam (Duk Amanar Dake Tsakanin Harshe Da Hakori Wataran Sai An Saɓa). 

 Baya da haka rarrashin juna a tsakanin masoya wata shinphiɗa ce dake ƙara kusanta zuciyoyin masoya.

Zakaga a soyaya so da yawa a duk lokacin da masoya suka sami wata matsala.

Idan har Allah yasa suka sami sasanci a tsakanin su se kaga sunkama ma amala fiye da yadda sukeyinta a baya.

Wannan shine yake nuna cewa soyayyar da sukeyi aoyayyace tagaskiya babu karya a cikinta.



A duk lokacin da ka/ki kasami matsala da da saurayinki karki taba barin wata dama dazata sanyaku yin fushi a lokaci daya.

Sabo da hakan bakaramar illa bace ga masoya idan ba'ayi wasaba wllh ZA'AYI dana sani.

Sannan Rarrashi a soyayya babban jigone ga rayuwar ita kanta soyayyar yana da kyau masoya su sabarwa da kansu rarrashi da tausan zukatan junansu yayin da sa6ani ya gifta. Domin inganta rayuwar su a gaba (ta auratanya).

 "Maphiya yawan ma'aurata kanyi ƙoraphi cewa abokin rayuwar su baya iya rarrashin sa idan sa6ani yashiga tsakani,

musamman mata sunphi puskantar wanna matsala idan suka hadu da basaraken Namiji". 

"Dan haka nake daɗa jan hankulanmu musamman mu maza a yayinda kaje zance gun masoyiyarka,



 hirarka taphi karkata ga yadda zaku gina rayuwar auranku mai inganci, idan kun kasance ma'aurata wani mataki zaku dauka wajen ganin kun magance rashin phahimta a tsakanin ku.

 idan hakan tapharu, kuma wani mataki zakubi dan magance pharuwan hakan, ko kuma wani hanya zakubi wajen gujewa pharuwan hakan". 

 ```Allah ya datar damu```

 Allah yajiƙan Mahaiphiyata da rahama Ubangiji ya kyautata makwanci, ya jiƙan duk kan musulmi baki ɗata.

KU SAURAREMU A CIKIN SHIRI NA GABA WATO SAKON SOYAYYA PART 6.

DAGA NI NAKU SANATAN MASOYA.......

MUNGODE 🙏

Post a Comment

Previous Post Next Post