WANENE MIJI NA GARI??

 MIJI NAGARI ... KO KUNSAN WAYE MIJI NAGARI 



Most of the time a wajen wa'azozi ko lectures ba a cika fadawa mutane halayen miji nagariba abin yana yawan bani mamaki akan meyasa baacewa ga halayen miji nagari, sai dai ayita cewa halayen mace tagari.... Ga wassu daga cikin halayen miji nagari Shine wanda yake ciyar da iyalinsa halaliya idan shima yaci... Yake shayar dasu idan shima yasha.... Kuma yake tufatar dasu idan ya suturta kansa bawai sai shekara shekaraba domin yasan darajar kwalliyar.... Shine wanda zai zamo zaki a waje, damo acikin gida wato me hàkuri ga dukkan lumura... Ko kuma yazamto kamar air condition wato a waje yake kara amman aciki sanyi yake bayarwa.... Shine wanda ya hada wassu siffofi guda 10 wadanda Allah Ta'ala Ya ambacesu acikin suratul Ahzab aya ta 35. Miji nagari shine wanda yakeson matarsa bayan aurensu fiyeda yadda yasota a layi ya nuna mata kauna ya jata ajiki ya sanar da ita abinda yafi faranta masa rai ya bata Abinci a baki ya tarairayeta kamar jaririya cikin so da kauna... Shine mai kishin matarsa. Domin Sayyidil waraa Sallallahu alaihi wasallam yace: "duk wanda baya kishin matarsa bazai shiga aljannah ba". Shine wanda ya dauki aure amatsayin Ibadah, ba wai abin wasa ba ko kuma abin jin dadin rayuwa kawai ba.... Shine wanda ya dauki matarsa amatsayin abokiyarsa, kanwarsa, almajirarsa, kuma abokiyar shawararsa. Shine wanda ba ya zagin matarsa, baya cin mutuncinta, ba ya cin zalinta, baya ha'intarta koda a bayan idontane...... Shine wanda yake zaune da iyalinsa cikin amana da gaskiya da kyautatawa ba cuta ba cutarwa. Shine wanda idan ya fahimci halayen matarsa, yake hakurin zama da ita tare da kyautatawa domin neman rahamar Allah Ta'ala. Shine wanda idan zai yi magana da matarsa, zai fadi gaskiya babu yaudara ko karya acikin ayyukansa da zancensa. Shine wanda ya dauka a zuciyarsa cewar: Iyayen matarsa, Iyayensa ne. 'Yan uwanta ma 'yan uwansa ne. Danginta ma danginsa ne. Shine wanda yake daukar cewa farincikin matarsa shine farincikinsa. Kuma Problem dinta, shima nasa ne... Shine yake kokarin kiyaye sirrin matarsa, kuma yake kokarin Kare mata mutuncinta koda awajen 'yan uwansa ne, tare da hikima da.fahimtarwa. Shine wanda baya fifita matarsa akan 'yan uwansa, kuma baya tauye mata darajarta. Yana ba ma kowanne gefe nasa hakkinsa kamar yadda shariah ta tanadar Shine wanda ya tanadi ruwan afuwa da hakuri acikin zuciyarsa domin ya rika kashe wutar tashin hankali da bacin rai aduk lokacin da hakan ta faru tsakaninsa da matarsa. Shine wanda a kullum yake kokarin tarbiyyantar da iyalinsa akan rayuwar addinin Islama ba rayuwa irinta yahudu da nasaraba Shine wanda yake zaune da matarsa komai da'di komai wuya ba zai dena nuna mata soyayya ba wai don tafara yankwanewa ko kuma karfinta yafara raguwa. Shine wanda yake bawa matarsa compliments a duk lokacin datayi kwalliya ko kuma tayi girki komai rashin dadinshi. Miji nagari baya raki,baya ihu don yaji abinci yayi yaji ko gishiri yayi waya. Sai dai yace: "uwargida abincinnan yayi dadi iyaka, sai dai gishiri yayi mana shisshigi aciki".... Shine Wanda yakeda tausayi a duk lokacin damatarsa bata da lfy to shima bashida lfyr yana tausaya mata matuka yakan dauketa da kanshi ya kaita asibiti domin tausaya mata... Kunji kadan daga cikin halayen maza nagari.... Allah Yasa mazaje su gane, su sauke hakkinsu na kulawa da iyali, su daina ha'intar matansu, su daina yin dare a layi, ko kuma cin abinci a rumfar me shayi... Ya Allah ka bamu maza nagari... Su kuma ka basu mata nagari ameen...

Post a Comment

Previous Post Next Post