YADDA ZAKA BAYYANA SOYAYYAR KA A GURIN BUDURWA.

 YADDA ZA KA BAYYANAR DA SOYAYYARKA. A GURIN BUDURWA.



“Wata yarinya na gani na kuma kamu da sonta, kuma ina zuwa gidansu, yaya zan yi na bayyana mata ina son ta?”

AMSA.

Zata iya kasancewa babba ce ko ‘karama, to koma dai yaya take a karon farko akwai bu’katar kafin ka furta mata da baki, kake nuna mata wasu alamomi da zasu ke bayyana mata hakan a zahiri. ta hanyar fifita ta fiye da sauran ‘yan gidansu.

Idan ka tashi zuwa gidan da wata tsaraba ko wata kyauta ya kasance tata ta fi ta kowa yawa. Idan salla ta zo ka d’inka mata kayan salla da takalmi da sauran kayan kwalliya na mata dai-dai ‘karfinka ka aika ko ka kai mata su. A lokacin azumi kake aika mata da kayan shan ruwa.

Idan ka je gidansu ko da bata nan kake tambayar ina ta tafi, idan kuka had’u ka sanar da ita ka je gidansu dan ka gan ta ku gaisa amma sai aka samu akasi baku had’u ba, kuma baka ji dad’in rashin ganin nata ba.

Kake yawan jan ta da hira, kake bata labarai masu sanya nishad’i da d’ebe kewa a dukkan lokacin da kuke tare.

Na tabbata ko baka furta kalmar so a gare ta ba za ta sha’ku da kai, za ka ke burge ta, za ta ke son ganin zuwanka, haka kuma ‘yan gidansu za su fahimci ‘kudurinka na kana sonta.

Bayan an shafe tsawan wani d’an lokaci hakan na faruwa, sai ka ware watarana ka ziyarce ta har gida ka aika a kirawo ta ka sanar da ita batun da tuntuni take tsammanin ji daga wajenka, wato na kana son ta.

Zaka iya sanar da ita ta hanyar tura mata da sa’ko ko akasin haka, amma zuwa da kai, ya fi sa’ko.

Idan kuma yarinya ce zaka sanar da ita hakan ne bayan ta kai munzalin tsayawa da samari. Dama tintini ‘yan gidansu sun dad’e da sanin manufarka a kanta, har ta kai suna zolayarta da kai, wata’kila ma suna yi maka magana akan hakan ko kuma sun zuba ido suna jiran ka furta hakan da kanka.

Daga nan kuma sai a shiga mataki na biyu wato fagen soyayya.

Post a Comment

Previous Post Next Post