KALAMAN DAKESA BUGUN ZUXIYA A SOYAYYA.
Kalmomiuku na yin sanadin karuwar bugun da zuciyata ke yi, kalmomi uku na sanya kafata karkarwa, kalmomi uku na sanya kaina ya yi ta faman rangaji, bari dai na furta su yau a gare ki ko na huta da azalzalar da zuciyata take yi mini a dangane da hakan, kalmomi uku: INA SON KI!!!
KECE ABAR TINANINA.
Damuwa? A’a sam, tayaya zan kasance cikin damuwa bayan a ko yaushe ke ce abar tinani na? Da ke nake kwana sannan kuma da ke nake tashi a cikin zuciyata. Ina kaunar ki!!
FUREN SOYAYYA.
Idan har ya kasance zan ke samun kyautar furanni a dukkan lokacin da na hadu da ke, to kuwa ni zan kasance mai ziyartar dausayi ma’abocin firanni masu kamshi na mallaka dukkan lokacina na wannan rana domin girmamaki. Ina son ki sosai a cikin zuciyata.
NA MALLAKA MIKI ZUCIYATA.
Ina tsananin so da kaunar ki bayan da kika samu nasarar sace zuciyata. Wannan zuciyar da ta kasance mallakina, ina mai farin cikin na mallaka miki ita a matsayin wata kyauta ta musamman. Na zama mallakin ki. Ki kasance mai ririta soyayyar mu kamar yadda na kasance. Na baki amanar kaina ki amince mu damke amanar juna. Ki huta lafiya.
AMSARTA NAKE JIRA.
Duk da Iskar dake kadawa a wajen lokaci bayan lokaci amma kasantuwata a bakin kogin bai hana gumi tsatstsafowa daga cikin fatata ba.
A zaune nake kan daya daga cikin duwatsun da suke gefen kogin ammafa kaina a sunkuye yake tamkar wanda aka bawa aikin irga korayen ciyayin dake wajen, fuskata cike take da damuwa.
Sautin shigowar sako wayata ne ya sanya na zabura na daukota daga cikin Aljihuna, sunan wadda ta turo da sakon da na gani ne ya sanya na yi murmushi cikin zumudi na shiga karantawa kamar haka ” Dan-Hausa ka yi hakuri a bisa jinkirin da na yi wajen turo maka da amsar sakon ka na ganin na amince da soyayyar ka. Abba a tun ranar da na fara dora ido na a kanka na ji zuciyata ta kamu da son ka, bana iya bacci a kullum idan ban ganka ba, kaine masoyina na hakika tunda har zuciyoyin mu sun aminta da juna. Ina son ka kaima kana sona ina yi maka albishir din ka samu makullin bude DAUSAYIN SOYAYYAr zuciyata, ina kuma fatan zaka kara shiri domin fantsama a cikin kogin soyayya mai dadi. Ina yi maka fatan samun nasara a dukkan al’amuran ka, daga masoyiyar ka SAFIYYAT.” ina gama karantawa ban san lokacin da na yi wani tsalle ba na fada cikin wannan kogin dake gabana saboda tsabagen farin ciki tare kuma da sanyawa a raina wannan shi ne kogin soyayyar da take magana a kai, ina cikin kogin bakina na furta kalmar SOYAYYA! SOYAYYA!! SOYAYYA!!! MAI DADI!