AMFANIN NAMIJIN GORO AJIKIN DAN ADAM

 Amfanin Cin Namijin Goro



Binciken masana a jami'ar binciken magunguna na kasa da ke Lagos dangane da amfanin da cin namijin goro ke yi a jiki ya nuna cewa:


1. Yana magance matsalar ido.


2. Yana kara lafiyar huhu, koda da hanta.


3. Yana maganin tari, mura, massara, gudawa, yawan atishawa, tarin fuka.


A wani bangaren an kara bayyana cewa:


4. Yana kara taushin murya ta hanya washe makogoro.


4. Yana karya guba a cikin jiki.


5. Yana karya kwayan cututtuka da ke cikin abincin da aka ci.


6. Yana maganin zazzabi.


Binciken na Dr Bartholomew Brai da Dr Emeka Amaechi daga jami'ar binciken magunguna na kasa da ke karamar hukumar Yaba ta jihar Lagos dangane da namijin goro ya kara bayyana musu cewa babu wani illa da cin namijin goro ke kawo wa jiki.


Madogarar mu ta kamfanin dillancin labari ya bayyana cewa masana sun bayyana cin namijin goro zai iya hana magani wani majinyaci ke sha aiki sosai a jiki wato ya kan ya ke masa kaifin aiki da ya ke yi a jiki.


Post a Comment

Previous Post Next Post