HIKIMOMI DA MEGIDA ZEBI YA KYAUTATAWA MATARSA

 Hikimomi da dabarun da maigida zai bi ya kyautata wa matarsa



Babu macen da ba ta son mijinta ya rika ji da ita, yana nuna mata soyayya da girmamawa. Yin haka na kara wa mace jin ta fi kowace mace ko jin ta a saman duniya, sannan duk yarintar mace ko tsufanta tana son mijinta ya rika daukarta a matsayin ’yar karamar yarinya, wadda na taba bayani a kan hakan. Ma’ana ya rika kula da ita kamar yadda zai kula da karamar yarinya, ya rika tunawa da kuruciyarta da ya sani a da kafin ya aure ta.
Saboda haka idan ba ka yin haka, to daga yau ka fara, don matarka ta rika jin ita ma ta kai mace, ta samu farin ciki da jin dadin zaman aure. Na tabbata yin hakan na bayar da kwanciyar hankali a cikin gida, sannan yana kara dankon soyayya sosai.
Ka rika kula da irin sabon kayan da take sa wa ko wani sabon abu da ta canja, kamar yin kitso, kunshi da kwalliya sai ka yaba da nuna burgewa a tare da kai. Duk wani sabon canji da ka gani yana da kyau ka san da shi, idan na yabawa ne, ka yaba, idan kuma na magana ne ka yi. Wannan shi ne zai kara tabbatar mata da cewa kana damuwa da ita.
Kalmar yarinta kada ta rabu da bakinka, kamar Bebita, ka rika sa wa tana jin a kullum ita ’yar karamar yarinya ce a wurinka. Wani lokacin ma ka kira ta da sunan da ka san babanta ko babarta suke kiran ta da shi a lokacin da take karamar yarinya, sannan ka fada mata kalaman yabawa masu dadi da cewa tana da kyan tsari.
Sai kira in ka fita ofis, ka kira matarka duk lokacin da ka kai ofis. Sai ka fada mata cewa: “Na kira ne don in tabbatar da jin lafiyarki.” Yin hakan na sa ta san cewa tana da muhimmancin gaske a wurinka sosai.
Wata rana ka ba ta hutun shiga kicin, kamar ranar da babu aiki, sai ka shiga ka dafa abincin da za ku ci ko in ba zai yiwu ba sai ka fitar da iyalinka wani wurin birgewar da za su dade suna tunawa. Zuwa sayayya tare ko zuwa wurin hutu da shakatawa, ka rika kulawa da ita kamar kwanan nan ka hadu da ita, wato kamar wata sabuwar budurwarka.
Kulawa ta musamman, idan tana son yin magana da kai, ka juya ka saurare ta da kyau. In kana karatun jarida ko kallon talabijin sai ka rufe. Haka in an bugo waya kuna cikin tattaunawa, kar ka dauka ko kuma ka kashe kafin ku fara tattaunawa. Ka saurare ta da kunnen basira kamar yadda kake yi da in ka je zance. Sannan ka rika nuna alamun kana ji da kyau ta alamun gyada kai, murmishi ko amsawa. Sauraren abin da mace ta fada na daya daga cikin abin da ke sa wa ta kara girmama ka.
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki. Ka sanya ta ji kamar ’yar yarinya karama a kirjinka. Ka bar ta har ta yi barci daga nan ne za ka gane irin baiwar da Allah Ya yi mata da kyanta da kai kanka baiwar da Allah Ya ba ka.
Zama a gida ranar da babu aiki don kawai ka kasance tare da ita, sannan ta san kana tare da ita ne ba don kamai ba sai dan kana son ka zauna da ita. Ka yi hira, wasanni, maganganun da za su sa ta ji dadin wannan kasancewar da ka yi da ita, tun da na sha ganin matan da ba su son mijinsu yana gida sai in lokacin da zai yi barci.
Yana da kyau wata rana ma ka kulle ta a daki, don kar yara su dame ta sannan kar ka bar su su shiga har na kamar tsawon awa shida, kawai don kana son ta yi barci ta huta. Sai kai ka kula da yara na dan wannan lokacin, ka fahimtar da su cewa innarsu na bukatar hutu, bari ita ma ta dan ji dadin rayuwarta. Sai ka yi girki ka kai mata daki ta ci gaba da hutawarta, babu abin da yake sa a ji dadin soyayya face irin wadannan abubuwan. Na san wani zai ce shi yaushe yake da lokacin hakan, ko ya ce in ya yi haka ai ya bayar da kansa ga matarsa, za ta raina shi. Wallahi babu maganar raini, tun da wanda aka yi duniyar ma dominsa na tabbata kowa ya sami labarin irin was an da yake da iyalinsa. Saboda haka ka zama miji nagari.
 
Ka matso da ita kusa da kai balle ma lokacin da ka san ta tara gajiya ko lokacin da take fushi ko take cikin bacin rai, kwantar da ita a kirjinka na iya sa wa ta dan huce ko ta samu sauki.

Post a Comment

Previous Post Next Post