Kalaman Da Ke Tausasa Zuciyar Masoya.
Hakika akwai kalamai masu dadin gaske dake tausasa zuciyar masoya.
Kuma kalaman sun kasance suna da matukar tasiri ga zuciyar maza ko mata.
Hakika a bangaren soyayya idan ka kasance kana da kalaman soyayya masu dadi a bakinka zaka dade kafin wani saurayi yazo ya kasaka a gurin budurwa.
Kema yanada wahala kisamu wata ta saye zuciyar masoyinki koda da kudi
Ba sai soyayya kadai ba, daddadan kalamai babban sinadari ne na iya zama da jama’a. Shiyasa ake cewa baki shi ke yanka wuya.
Idan ki ka iya lafuza masu dadi, to za ki ci ribar soyayya.
da kuma uwa uba ribar zama da miji. Amma ki rika yi wa masoyinki ko mijinki kalamai kamar na irin wanda gandurobobi ke yi wa ‘yan fursuna,
ke ma kin san mijin ki zai ga kamar kina so ki zama ke ce oga kenan.
A rayuwa ta zaman soyayya da kauna, idan mai gida yana magana, ki kasance kin fi shi iya zaro kalamai na kwantar da hankali.
idan kuma shima ya iya, to zama zai kara yin daidai kenan.
Ki tuna shi dan adam yana so ya ji ana yabonsa.
Ki duba mana ki ga mawaka, ai da abu biyu suke cin ribar bakin su. Na farko su kambama mutum ya ji dadi ya ba su kudi,
na biyu kuma su yi wa wani zambo ya ji haushi. Sun cewa mu- tum gwanki, dan giwa kai har toron giwa suna kiran wanda suke kambamawa.
To ku masoya don me ba za ku rika yarfa wa juna dadadan kalaman kwantar da zuciya ba.
Ana so a rika yi wa masoyi ko masoyiya kalamai na kambamawa,
amma ba na yaudara ba.
ba a ce sai kin masa waka ko sai ka yi mata waka ba. Shin ba ku iya kalaman tausasa zukatan juna ba ne?
Kada ku tsaya kuna kwaikwayon abin da wani ko wata suka rubuta a littatta- fai. Ku kirkiro na ku mana.
Ga wasu da na ci karo da su a wani wuri zan kawo maku.
Ban fa ce sune dadadan ba, amma dai ina so ne su zamo matashiya ga masoya domin su rika dan zakulo wa junansu kalamai musamman irin na begen nan idan ba su kusa, ko dayansu ya yi tafiyar da zai dauki kwanaki kafin ya dawo.
Na san idan wasu sun karanta, za su ce wanda ya tsara wadannan kalaman bai ma cika gwanin soyayya ba, dan tagajan-tagajanne.
To kai ina nakan suke?
Sai ka zakulo su ka dan rika jefa wa sahibar taka.
Cikin makon da ya gabata, ina zanune ina rubutu, sai wata Qawata ta yi min sakon tes a waya ta, ta ce min ga wasu kalamai ta tsakuro daga cikin wani gidan intanet, wanda wani ya tattara.
Ta ce min gidan intanet din mai kama da ‘blog’, sunansa.www.lambunqaunah.com.ng
* Zuciyarki ta zama takarda, tawa ta zama biro in rubata miki shafin kauna !
* Ki zama kofa na zamo makulli, mu hadu mu bude dofar soyayyar lambun zuciyata!
* Na kasa tsaye na kasa zaune a lo- kacin da na fara ganinki a cikin taro, kin fita daban kaman wata a daren sha biyar!
* Ya madarar zuciyata, ki zamo si- minti in zamo bulo mu gina gidan k uana a filin soyayya.
* Watau yau da na tashi, sai na ga rana ta taso ta haske garin nan, amma duk hasken ta ba kai hasken fuskar da ta haske zuciyata ba, domin ni a zuciyata hasken fuskar abin kuana ta ya fi duk hasken rana.
* Ki zama fetur na zama inji mu hadu mu tada lantarkin kauna.
* Ya sahiba ta na ba ki filin zuciya ta ki shuka a duk wani lungu da sakon bishiyar so da kauna don mu sami in- uwar da za mu zauna mu yi soyayya.
* Ke ce madubi abar dubawa ta duk safiya, kin zamo min tamkar fetur a mota, rayuwa ta ba ke lami ce ya rabin raina.
* Ke ce makwarariyar madarar zuciyata, wadda da na sha za ta has- kaka zuciyata ta yi fari.
* Rayuwata babu ke tamkar wayar da ba wayar caji ce ba, kuma babu layi, a mace ba amfani.
* Kunne na ya kurmance saboda rashin jin kalaman kaunarki kullum, baki na ya daina magana daidai sa- boda rashin begen zumar rayuwata kullum.
* Ta tsagwaron zallar tsabar kwayar tsokar zuciyata, idona zai makance saboda rashin ganinki a yau da kullum.
* Ya gangariyar madarar zumar da ba ta da gauraye, ya tauraruwa a cikin jinsin taurari mai haske zuciyar masoyinta.
* Idona ya bude ya ga haske irin na walkiya don ya ganki. Ziciyata na shan lagwadar zuma da mada kauna.
* Idon basira lafazin rayuwata.
* Alfijir na kauna ya keto, tsuntsayen soyayya sun tashi suna yawo a sararin samaniyar zuciyata.
* Ya fankar da ke juya zuciyata, zan zamo kwalekwale, ki shigo mu hau kan kogin so, in zamo katifa ki zamo gado a cikin dakin kauna.
* Hadarin begen ki ya hado, gugu- war sonki ta taso, sai ruwa mai karfi ake yi na kaunarki a filin zuciyata.
A hakane zakubi kuna zakulo naku zafaran kalaman zaku iya yin wadanda sukafi wadannan dadi idan har kuna jarabawa.
Karku taba mantawa dawani abu guda 1 matsoraci baya taba zama gwani
A matsayinku na masoya dilene se kun cire wadannan Abubuwa kamar haka....
*Kunya
*Tsoro
Idan akace tsoro ananufin karka taba jin tsoron cewa zakayi ko zaku fada ayimuku dariya ko a inane.
Idan akace kunya ana nufin kar ka taba yin nauyin baki wajen furtawa masoyiyarka kalaman so da kauna
Domin idan wani yazo yafika kalamai ze kwacemaka budurwarka A saukake
Duka duka anan muka kawo karshen wannan sakon namasoya,
Kujiramau kuma zuwa sako nagaba MUNGODE 🙏