KALAMAN SOYAYYA NA MA'URATA NA MA’AURATA ZALLA
Miji:
INA SON KI!
Ba zan iya musa
lta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana. Ina son ki matata. Babu wani abinci da yake yi min dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai dad’i. Ki kula min da kanki.
ZUCIYA TA NA CIKE DA KEWARKI MATA TA.
Mata ta uwar ‘ya’ya na. Na kan yi kewarki sosai a dukkan lokacin da na duba gefe na ban gan ki ba. kamar kullum, yanzu haka ina zaune cikin tinaninki. Zuciya ta na cike da kewarki, zan samu sassauci ne kawai idan na ji ki a kusa da ni. Ki kula min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawarki ta dawo hannu na. Ina Son Ki.
BA NI DA KAMAR KI.
Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna. Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
Mata:
INA ALFAHARI DA SAMUNKA.
Hasken idaniya ta, annurin rai na. Miji na, uban ‘ya’ya na. Tabbas samun miji irinka shi ne abun da mata da yawa suke fata. Na same ka hakan ya sanya nake jin tamkar na fi kowace mace sa’a a duniya. Ina fatan dawowarka gida lafiya, miji na abun alfahari na.
KAI NE NAKE GANI NA JI SANYI A ZUCIYA TA MIJI NA.
Ina fatan kana nan lafiya miji na? Ina nan zaune cikin gida amma zuciya ta tana tare da kai. Kai ne kawai nake gani na ji sanyi a cikinta. Ina nan ina jiran dawowarka gida lafiya. Ina son ka. Ka kula min da kanka.