DOMIN MA'AURATA ZALLA 🧏🧏🧏
MAGANIN BUSHEWAR GABAN MACE.
Hakikanin gaskiya wannan ba karamar lalura bace ga maaurata.
Domin lalurace wacce zata kawowa mace nakasu a bangaren zamantakewa na Aure.
To amma a yau munkawomuku mafita kala daban daban akan wannan matsalolin naku.
gamai samun daukewar ni'ima da rashin sanin dadin aure ko rashin nishadi to amarya ko uwar gida ga yanda zaki magance wadannan matsaloli cikin sauki, sai ki samu:
-aya
-zuma
-dabino
-garin sallaja
sai ki markadesu ki tacesu sai ki rinka diba kadan-kadan kina hadawa da zuma da garin habba kadan kina sha safe da yamma, wadda batayi aure ba kada tasha.mijinki zai ji kin canza sosai.
● SIRRIN MA 'AURATA:●
shi wannan wani sinadarine mai albarka wanda ake yi masa lakabi da sinadarin ma'aurata, kuma yana jimawa a jiki, sannan yana kara kuzari kuma yana karawa mace martaba ga mijinta, zaki samu:
-furen zogale
-zanjabil
-habba
-garin raihan
sai ki dakesu guri daya sudaku dakyau sai rinka diban karamin cokali kina hadawa da zuma kina safe da yamma shima wannan sai mai aure amma idan kin kusa yin aure zaki iya yin wannan hadin.
HADIN MATAN MATAN SUDAN:
ko shakka babu shi wannan hadin matan masar da matan sudan,da matan jordan suna yinshi yana kara ni'ima musamman yana gyara aure, kuma yana kara dadi wurin saduwa yana kuma sa nishadin masoya, sannan kuma zaki zama yar gaban goshi
-kankana mai kyau
-zuma
-raihan
sai ki yayyanka kankanar ki zuba a kofi, ki saka zuma da madarar ruwa da garin raihan sai ki rinka sha safe da yamma.
RASHIN SHA'AWA:
akwai matanda basayin sha'awa ko basa jin dadin saduwa ko ni'imarsu ta dauke, to yanda za'a magance wannan matsala shine sai kisamu
-zangarniyar zogale,da ya'yanta gadaya
-karanfani
-citta
-masoro
-da kinba
sai ki dakesu guri daya su zama gari,sai ki rinka shan wannan hadi a shayi safe da yamma,ki gwada ki gani, yana kara dadin da mai gida zai gamsu sannan kuma zaki rinka cin dabino(ajuwa) mai kyau tare da kwakwa zaki sha mamaki.
NI'IMA SINADARI MAI DADI GA MAAURATA
ga wani hadi na musamman dan karin ni'ima da nishadi da dadi
-ya'yan zogale
-kankana
sai ki dakesu guri daya suyi laushi sai ki rinka sha da nono safe da yamma.
DON SAMUN CIKKAKEN FARIN CIKIN MA'AURATA.
shi wannan wani hadi ne da akeyinshi dan farin cikin ma'aurata, kuma yana sa asamu nishadi da kuma karin ni'ima da dadi, yanda akeyi shine za'a samu
-kankana mai kyau sosai( a yayyankata)
-ya'yan zogale
-kumasoriyya ta asali
-ayaba mai kyau sosai
ya'yan zogale da kumasoriyya za a dakesu da kyau suyi laushi, sai ki rinka diban karamin cokali na garin maganin kina hadawa da wancen kankanar da ayaba da madara ta ruwa, sai ki yamutsasu ki rinka sha, sau biyu a rana safe da yamma
sannan kuma in zaki kwanta da daddare sai ki hada farin miski da zuma farar saka da man zaitun mai kyau ki rinka shafawa a gabanki,zai kashe kwayoyin cututtuka da gamsar da maigida da nishadi.
Harkullum mudai fatanmu Agareku ku kasance masoyan gaske da kuma samun kyakkyawar zamantakewa.
Shine babban farincikin mu a rayuwa,kuci gaba da bibiyarmu zamuna kawomuku muhimman abubuwa.
Ananne muke cewa wassalamu Alaiku warhmatullahi wabara katuhu.