MU GYARA KUSIURENMU MA'AURATA MAZA DA MATA

 *MU GYARA KUSKUREN MU MA'AURATA*

DANNA NAN DOMIN KOLLON VIDEO KAI TSAYE 👇👇👇👇

NAN ZAKA DANNA DOMIN KOLLON VIDEO KAI TSAYE

👇👇👇👇👇👇👇👇

 Assalamualaikum inayiwa dukkan daukakin masoyan duniya da maurata gaisuwa baki daya.

A yau munzomuku da yadda zaku gyara zamantakewarku a matsayinku na maaurata

Akwai abubuwa da yawa wadanda Ma’aurata suke aikatawa a lokacin Jima’insu. Kuma wadannan abubuwan suna da illoli masu yawa dangane da lafiyarsu jikinsu ko addininsu.

Ga wasu ‘yan kadan Zan lissafo:

1_RASHIN GABATAR DA WASANNI KAFIN JIMA

Wannan ba daidai bane domin kuwa Manzon Allah (saww) yace “IDAN ‘DAYANKU YAYI NUFIN KUSANTAR IYALINSA, TO LALLAI A SAMU ‘DAN AIKE A TSAKANINSU”.

Sai Sahabbai suka ce “Wanne irin ‘dan aike?” Sai yace “SHI NE SUMBA (KISS) DA KUMA MUBASHARA (RUNGUMAR JUNA).

Rashin gabatar da irin wadannan wasannin yakan haifar da rashun gamsuwar Jima’i. Shi kuwa rashin gamsuwar Jima’i yakan haifar da matsalolin da zasu kawo rabuwar auren.

Yana daga cikin fa’idodin gabatar da wadannan

wasannin, zai sa Maniyyin ita Macen ya gangaro daga ainihin inda yake, sannan kuma za ta samu cikakkiyar gamsuwa.

2_KUSKURE NA BIYU SHI NE TSOTSON AL’AURAR JUNA

Wannan kuskure ne babba wanda ko dabbobi basu yinsa. Duk da cewa babu wata ayah ko hadisi wanda ya fito karara ya yi bayani akan haramcin wannan, to amma Malamai sun yi sabani sun kasu gida biyu akan hukuncin yin hakan, kuma sun raba hukuncin gida

biyu:

Idan har ya kai ga shan Maniyyi to Malaman Malikiyyah da Hanafiyyah sun ce HARAMUN ne. Domin su a wajensu Maniyyi najasa ne. Kuma bai halatta Musulmi ya shigar da najasa cikin cikinsa ba.

Idan kuma Maziyyi ne aka tsotsa, to dukkan Malamai sun ce HARAMUN ne. domin kuwa shi Maziyyi najasa

ne abisa ittifakin Malamai bai daya.

Idan kuma ba a tsotsi Maziyyi ko maniyyi ba, to Malaman da suke bayar da fatawa a Jami’ar Az’har sun ce MAKRUHI NE.

Wasu kuma irin su Nasiruddeen Albaniy sun ce HARAMUN NE duk da hakan.

3_KUSKURE NA UKU SHINE YIN SURUTAI A LOKACIN JIMA’I

Shi ma wannan ba daidai bane. Shari’ar addinin Musulunci ta hana mutum ya rika yin magana a lokacin da yake tsirara.

4. KUSKURE NA HUDU SHI NE RASHIN LULLUBE JUNA DA MAYAFI: Shima wannan ba daidai bane. yin hakan ya yi kama da Jima’in dabbobi kenan.

5_KUSKURE NA BIYAR SHINE RASHIN AMBATON ALLAH KAFIN FARA JIMA’I

Ya kamata Ma’aurata su kula da yin Bismillah tare da karanta addu’ar nan wacce Manzon Allah (saww) yace duk wanda yake karantawa yayin Jima’i da matarsa, to indai aka samu rabo, to shaitan ba zai iya cutar da yaron ba.

Ga addu’ar nan: “BISMILLAHI ALLAHUMMA JANNIBNASH SHAITAN WA JANNIBISH SHAITANA MA RAZAQTANA”.

6_KUSKURE NA SHIDA_

idan Miji ya biya bukatarsa, to bai kamata ya gaggauta sauka ba, har sai ita ma matarsa ta biya bukatarta.

7_RASHIN SAUYA YANAYIN KWANCIYA

Shi ma wannan ayar Alqur’ani ta bada damar miji ya sadu da matarsa bisa kowanne irin yanayi. A tsaye ko azaune ko a kwance ko a tsugunne, mutukar dai ba ta dubura

bane. Don haka ya halatta Ma’aurata su rika chanza yanayin kwanciyarsu saboda kara ma juna nishadi.

8_KUSKURE NA TAKWAS SHINE SADUWA A LOKACIN DA TAKE CIKIN JININ HAILA, KO JININ

HAIHUWA

Allah (SWT) ya ce : “KU NISANCI MATA A LOKACIN HAILA. KAR KU KUSANCESU HAR SAI SUNYI TSARKI”.

9_KUSKURE NA TARA SHINE SADUWA TA DUBURA

Shi ma wannan kazanta ce wacce ko dabbobi basu yi. Manzon Allah (saww) ya ce “TSINANNE NE DUK WANDA YA SADU DA MAI HAILA, KO KUMA YA SADU DA

MACE TA DUBURA”.

*KINA WA MIJIN KI SUMBA KUWA??? (KISS)*

*KISS YANA MATUKAR KARA SOYAYYA GA MA"AURATA* 

Amma a dinga wanke baki sosai saboda tsaro

*Ya ke uwar gida, ko amarya, ko kin san cewa yiwa mai gida ko ango sumba ya kansa hankalinsa ya dawo kanki kuwa.*

*To ki saurara kiji, yakamata kisan cewa sumba (kiss), yana da matukar muhimmanci mara misali a rayuwar aure, wajen kara dankon soyayya tsakaninki da mai gida.*

Dan duk lokacin da zaki yiwa mai gida sumba (kiss), zai ji a ransa ashe baki kyamar sa, kuma baki gudunsa, kema

kuma haka zaki ajeye a ranki in ya yi miki. Kuma yin sumba (kiss), sakanin ma'aurata, watau mata da miji, yana taka rawar gani wajen motsa sha'awan juna, kuma ita sumba (kiss), bawai sai a baki kadai ne kawai ake

yinta ba, ko ina a jikin mijin ki za ki iya yi masa, shima kuma miji zai iya sumbartar matar sa a ko ina a jikinta,

kamar su, fuskarta, bakinta, nononta, goshinta, cibiyarta.

Da dai sauran su.

Kuma yin sumba (kiss), alama ce dake nuna irin tsananin son da ma'aurata kema juna.

Ba wayewa ba ne, don matar ka tama sumba, sai kamata kallon yar iska, ko don mijin ki ya miki sumba ki masa

kallon da iska, to wallahi wannan jahilci ne, idan kuna ganin kuma kariya ne to sai a tambayi mallaman addi ni, aji

gaskiyar lamarin.

*DABARA TA ITACE YIWA MIJINA SUMBA(KISS)* 

kamar dai uwar gida ta tambayi marya cewa me kike yiwa mai gida ne naga duk hankalinshi ya dawo kanki sai tace sumba(kiss) saboda haka yake uwar gida yakamata kisan cewa kiss yana da matukar muhimmanci marar misali wajen kara dankon soyayya tsakaninki da mai gida dan duk lokacin da zaki yiwa mai gida kiss zai ji aransa

ashe baki kyamarsa kuma baki gudunsa kema haka zaki aji ranki in ya yi maki kuma yinsa yana taka rawar gani wajen motsa sha'warku, kuma ita kiss nan bawai sai baki da baki ne kawai ake yinta ba ko ina a jikin mijinki zaki iya yi masa, shima kuma miji zai iya kiss matarsa a ko ina ajikinta kamarsu.

NONONTA,

BAKINTA,

FUSKARTA,

GOSHINTA,

CIBIYARTA,

DA DAI SAURANSU;

kuma yana daga cikin manya-manya abubuwanda ke kara dankon soyayya tsakanin mata da miji da kuma motsa sha'awa,kuma alama ce dake nuna irin tsananin son da kikewa mijinki shima kuma haka lalle wannan ba karamar dabara bace,ki jaraba uwar gida zaki dace da yarda Allah.

*ABIN LURA*

mata da yawa suna manta wanna bansan ko kunya bace tasa bata kiss kiss yanada amfani ga miji yar'uwa inda bakiyi ki gwada koda sau daya ne zaki sha mamaki.

Harkullum mudai fatanmu Agareku ku kasance masoyan gaske da kuma samun kyakkyawar zamantakewa.


Shine babban farincikin mu a rayuwa,kuci gaba da bibiyarmu zamuna kawomuku muhimman abubuwa.


Ananne muke cewa wassalamu Alaiku warhmatullahi wabara katuhu.


Post a Comment

Previous Post Next Post