SAKONNIN SOYAYYA GUDA 10+
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta, kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada. Na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
NA GOMA.
Abba ne zaune a kan wata farar kujerar roba cikin wani lambu mai d’auke da korayen ciyayi da ni’ima mai dad’i, wajen da ya zamo masa wajen hutawar shi a dukkan lokacin da ya fita wajen aiki bayan ya yi aikin ya gaji nanne inda ya saba zuwa ya kirawo matar shi a waya domin jin halin da ta ke ciki tun bayan auren su wanda hakan ba karamin burge matar tashi yake yi ba sannan kuma yana k’ara soyayyar shi a cikin zuciyarta.
Yauma dai kamar kullum, ya fito da wayar ta shi daga aljihu ya shiga kiranta, kamar jira ta ke yi dama bugu d’aya ta d’aga, bayan sallama sai kuwa ya shiga cewa da ita
“Matata Uwar ‘ya’yana maganin kukana, Salimat a baya kafin mu yi aure na yi tinanin cewa bayan mun yi aure ba zan ke samun kulawa da tarairaya tare da kalaman soyayyar nan ta ki masu dad’i ba, na yi zaton komai zai canja kamar yadda na ke gani a wasu gidajen auren ashe mu ba haka abun ya ke ba saima abun da ya ci gaba ya kuma sauya sabon salo mai dad’i, Salimat ina son ki, koda aiki nake yi yadda zan dawo gida na tarar da ke kawai na ke yin tinani, kuma koda abinci zan ci ina ci ne kawai saboda na rayu amma ba wai dan ina jin dadin shi ba, ina son ki sanar da ni abun da zan taho miki da shi idan zan dawo gida ki kuma kular min da kanki har zuwa lokacin da zan dawo kulawar ki ta dawo hannuna