SHAWARA GA MA'AURATA MATA
kiji tsoron Allah ki kula da mijinki, ki ba shi kulawa ta
musamman ki zama mai tsafta da iya ado, ki zamo mai kisisinar da gwalli, da rangwada duk hanyar da Zaki Bi , ta haka Zaki dauke hankalinsa ya daina kula yan'mata da zawarawa a waje.
amma kin kasa kula da shi kin kasa kula
da kanki, ba ki San me zai ja hankalin mijinki ba, kin zauna daga ke sai dauri iya kirji, ba wankin baki ba gyaran ga shi, ba kula da kafa ba wanki ba wanka ba aski hammatarki bare na gaba ( farji ) dole ki samu matsala don haka ki gyara in kina so ki ga dai-dai.s
hawara ga ma'aurata mata
Ki zamo mace ta gari ta kwarai ki zamo mai samawa mai gidanki farin ciki karki sa masa tashin hankali da bacin rai karki zagi mijinki karki yi abinda zai bata masa rai Musamman wajan kwanciya wasu matan suna azabtar da mazajensu ta wannan hanya wata in bai neme taba ba zata Kai kantaba wai ba aji waya gaya miki kyaje wajen Jan ajin matsa sha'awa ko bai niyyar yi ba yaji yana bukarta yayi kuma ta haka hankalinsa zai dawo jikinki ko yaushe yaji yana so ya kasance da ke ki kula garin Neman gira a rasa Ido.
shawara ga maza
ka nemi halali ka ciyar da ya'yanka da iyalanka ,ka sa halali ka tufatar da iyalanka da iyayenka da halali, kada kaci haramun ko kasa haramun ko ka ciyar da ya'yanka da iyayenka da haramun, Ku Sani, haramun tana lalata rayuwa, tare da Hana karbar addu'o'in don haka Ku gujewa duk abinda kuka San zai iya jefa Ku cikin fushin ubangiji.
SIRRIN MIJINKI
DOMIN KARIN NI'IMA
irin wannan hadin shine ake Kira sa maigida kuwwa yana matukar saurin kawowa mace ni'ima.
zogale.
zuma
nono.
ki busar da zogelenki amma ba a cikin Rana ba, ki daka shi Yayi laushi sosai Zaki iya tankadawa sai ki rinka dibar cokali daya kina zibawa a nono ki zuba zuma cokali (³) a ciki ki rinka sha wannan hadin yaaj matukar Kara wa mace ni'ima sosai da lafiya.
GYARAN JIKI
gyaran mace yana matukar muhimmanci a tare da ke yar'uwa kada ki Bari fatar jikinki ta koma tamkar ta wata tsohuwa.
ganyen dalbejiya.
lalle.
zuma.
man zaitun.
sabulun gana.
dudu osun.
ki hada su guri daya ki daka a cikin turmi mai tsafta, sai ki rinka wanke da shi Zaki ga yadda fatarki zata canza.
GYARAN GASHI
wacce gashin kanta ke yawan karewar sai ta samu man dalbejiya ba tare da kin hada masa komai ba kullum da dare sai ki rinka shafawa yana Hana zubewar gashi.