YADDA ZAKI KARAWA KANKI NI'IMA GIDAN NI'IMA

 GIDAN NI"IMA DON KARA WA KANKI NI'IMA



 ruwan kankana. kwai. zuma.

idan kika sami kankana Zaki tace ta, ki sami ruwan cikin karamin kofi sannan sai ki kawo kwanki guda daya sai ki fasa shi a cikin kananan, sannan sai ki kawo zumarki cikin babban cokalin biyu, sai ki shanye wannan yan'uwa muddin kuka daure da sha wannan to kuwa ina mai tabbatar muku zaku ga aikin.

SHAWARA GA MA'AURATA MAZA

ka zamo mutum mai nutsuwa kar ka sake ka rinka aikata abubuwan da zasu jawo maka zubewar mutuncinka ya kuma jawo zubewar mutuncin iyalanka kamar shaye- shayen , hakika shaye-shayen yana jawo raguwar kima da kuma yawan alfasha ya kasance ba ka da aiki sai zagi don akwai wadanda zagin ya zama musu Riga ya zame musu jiki, ko zance zasu yi sai sun hada da alfasha kunga ai wannan ba tarbiyar bace ta gari idan baka so ya'yan ka su dauka sai ka daina.

shawara ga ma'aurata mata

kiji tsoron Allah ki kula da mijinki, ki ba shi kulawa ta

musamman ki zama mai tsafta da iya ado, ki zamo mai kisisinar da gwalli, da rangwada duk hanyar da Zaki Bi , ta haka Zaki dauke hankalinsa ya daina kula yan'mata da zawarawa a waje.

amma kin kasa kula da shi kin kasa kula

da kanki, ba ki San me zai ja hankalin mijinki ba, kin zauna daga ke sai dauri iya kirji, ba wankin baki ba gyaran ga shi, ba kula da kafa ba wanki ba wanka ba aski hammatarki bare na gaba ( farji ) dole ki samu matsala don haka ki gyara in kina so ki ga dai-dai.


shawara ga ma'aurata mata

Ki zamo mace ta gari ta kwarai ki zamo mai samawa mai gidanki farin ciki karki sa masa tashin hankali da bacin rai karki zagi mijinki karki yi abinda zai bata masa rai Musamman wajan kwanciya wasu matan suna azabtar da mazajensu ta wannan hanya wata in bai neme taba ba zata Kai kantaba wai ba aji waya gaya miki kyaje wajen Jan ajin matsa sha'awa ko bai niyyar yi ba yaji yana bukarta yayi kuma ta haka hankalinsa zai dawo jikinki ko yaushe yaji yana so ya kasance da ke ki kula garin Neman gira a rasa Ido.

shawara ga maza

ka nemi halali ka ciyar da ya'yanka da iyalanka ,ka sa halali ka tufatar da iyalanka da iyayenka da halali, kada kaci haramun ko kasa haramun ko ka ciyar da ya'yanka da iyayenka da haramun, Ku Sani, haramun tana lalata rayuwa, tare da Hana karbar addu'o'in don haka Ku gujewa duk abinda kuka San zai iya jefa Ku cikin fushin ubangiji.


SIRRIN MIJINKI

DOMIN KARIN NI'IMA

irin wannan hadin shine ake Kira sa maigida kuwwa yana matukar saurin kawowa mace ni'ima.

zogale.

zuma

nono.

ki busar da zogelenki amma ba a cikin Rana ba, ki daka shi Yayi laushi sosai Zaki iya tankadawa sai ki rinka dibar cokali daya kina zibawa a nono ki zuba zuma cokali (³) a ciki ki rinka sha wannan hadin yaaj matukar Kara wa mace ni'ima sosai da lafiya.

GYARAN JIKI

gyaran mace yana matukar muhimmanci a tare da ke yar'uwa kada ki Bari fatar jikinki ta koma tamkar ta wata tsohuwa.

ganyen dalbejiya.

lalle.

zuma.

man zaitun.

sabulun gana.

dudu osun.

ki hada su guri daya ki daka a cikin turmi mai tsafta, sai ki rinka wanke da shi Zaki ga yadda fatarki zata canza.

GYARAN GASHI

wacce gashin kanta ke yawan karewar sai ta samu man dalbejiya ba tare da kin hada masa komai ba kullum da dare sai ki rinka shafawa yana Hana zubewar gashi.


Post a Comment

Previous Post Next Post