Dalibai 'yan Najeriya a Sudan na neman a kwaso su daga kasar.
21 Aprilu 2023
Kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a kasar Sudan ta bukaci mahukuntan Najeriya su kwaso su daga Sudan zuwa gida Najeriya.
An shafe kwana shida ana ba-ta-kashi tsakanin sojojin gwamnatin Sudan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) a kasar tun da aka fara yakin a ranar sha biyar ga watan Afirilu.
*3 SIMPLE WAY HOW TO MAKE $100 A DAY*
*CLICK HERE* 👉👉👇👇 https://shorturl.at/nzHN9👈👈
*DON'T FORGET TO SHARE TO ANOTHER GROUP*
Kungiyar daliban ta fitar da wata sanarwa, waccce ta nuna damuwa game da rikicin da ake fama da shi a kasar ta Sudan.
Shugaban kungiyar Abubakar Babangida ya shaida wa BBC cewa daliban suna cikin mawuyacin hali.
"A halin yanzu babu zuwa makaranta sannan shaguna na nan a kulle, wasu unguwanni ba su da wuta kuma ba su da ruwa muna zaman cikin gida kullum a gidanma muna cikin tashin hankali" in ji Abubakar Babangida.
Shugaban kungiyar daliban na Najeriya da ke Sudan din ya ce su na jin karar bindigogi da kuma jirage daga cikin gidajensu.
Ya ce sun tuntubi ofishin jakadancin Najeriya da ke Khartoum kan batun mayar da su Najeriya amma babu wani labari.
Ya kara da cewa babu wani dalibi dan Najeriya da ya mutu ko ya ji rauni a sakamakon rikicin na Sudan ya zuwa wannan lokacin.
Abubakar ya ce tuni dai wasu kasashen nahiyar Afirka ciki har da Uganda suka bayyana aniyar kwashe dalibansu.
Fada ya kaure ne a tsakanin rundunonin sojoji biyu na Sudan din wadanda a baya abokan juna ne.
Zuwa yanzu dakarun Rapid Support Forces sun sanar da tsagaita wuta na kwana uku.