Allah Sarki Daga Zuwa Raba Fada Matashi Mai Shekaru 23 Ya Hadu da babbar Jarabawar Rayuwar sa

Allah Sarki Daga Zuwa Raba Fada Matashi Mai Shekaru 23 Ya Hadu da babbar Jarabawar Rayuwar sa

 Allah Sarki Daga Zuwa Raba Fada Matashi Mai Shekaru 23 Ya Hadu da babbar Jarabawar Rayuwar sa

Ina sana’ar dinki, na tashi tunda sassafe ina ta farinciki, ba abunda kemin ciwo a rayuwa. sai naje kasuwa wurin sana’a ta domin cigaba da aiki.

Awannan ranar har dare nakai ina aiki misalin karfe tara 9:00pm sai na rufe shago mukaje dani da maigidana domin mukai kayan da mukagama dasu. Ina zaune sai naji hayaniyar mutane awaje.

 Bayan nafita sai natarar da mutum biyu suna fada, nan take nashiga tsakiyarsu domin rabon fadan.

Kawai sai dayan ya zaro wuka ya caka mun a hannu ganin yanda jini ke zuba sosai, sai suka gudu.

Aka kaini assibitin Dala domin ayimin aiki, likitan yace sai ancire hannun domin kuwa jijiyar jinin hannun ta tsinke.

 Ahaka ne Allah ya jarrabani da rashin hannu daya, daga wurin aikin alkhairi (Rabon Fada) tsakanin mutum biyu domin sulhuntasu.

Ina neman addu’a da taimakon ku yan uwana maza da mata, ina fatan Allah ya kare mu daga dukkan mummunar kaddara. Ameen

Post a Comment

Previous Post Next Post