Rahotanni daga jihar Kano na cewa wani matashi mai suna Isyaku mai Baro ya ƙi yarda ya karɓi kyautar kamfanin buga ruwan Pure-Water da tsabar kuɗi Naira Miliyan 20 da kuma motar hawa ta kimanin Naira Miliyan 4 da ginanne gida a GRA Kano don ya rabu da Budurwar sa kamar yadda abokin karawar sa ya yi masa tayi.

Alhaji Abubakar Mai Shadda wani hamshaƙin attajiri ne dake saffarar kaya daga Dubai zuwa Najeriya shine yaga yarinyar taje siyayya tare da ƙawayenta a ɗaya daga cikin kantunan sa a daren jiya inda yace yana sonta kuma ya nace yayin da shi kuma saurayin yarinyar sana'ar tura baro yake a kasuwar Kantin Kwari kuma gobe Juma'a za'a ɗaura musu aure da yarinyar.
Rahotanni sun ce yanzu haka ƴan'uwa da abokan arziƙi na can suna tausar ƙirjinsa a kan ya janye wa Alhaji Abubakar ya haƙura ya nemi wata saboda dukiyar da za a ba shi ko mata huɗu yake so zai iya aura duk a goben amma ya kafe kan cewa mutuwa ce kawai zata raba shi da ita saboda haka ko duka dukiyarsa zai ba shi ba zai karɓa ba yafi son Maryam ɗinsa, shima uban yarinyar yace ba za'a fasa auren ba sai dai idan shi Isyakun ne yace ya fasa.
Kunji fa masoyi na gaskiya ko zaka iya yin irin wannan soyayyar ta matashin nan?